'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, da fadar shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan wakilan Najeriya dubu 1 da 411 a taron sauyin yanayi na kasa da kasa da ke gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.
‘Yan Najeriya da dama sun soki yawan wakilan Najeriya, wanda shi ne na uku mafi yawa a taron na duniya, a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan kasar ke fama da matsalar tattalin arziki sakamakon manufofin gwamnati.
Obi a ranar Lahadi, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya taya Najeriya murnar samun adadin tawaga irin ta kasar Sin, yana mai cewa kasafin kudin kasar Sin na shekarar 2024 ya kai dala tiriliyan 4 inda aka ware dala dubu 2,860 kan kowane mutum, Kasafin kudin Najeriya kuwa ya kai dala billiyan 33..
Ya yi nuni da cewa, Nijeriya ta fi kasar Sin yawan mutanen da ke rayuwa cikin talauci duk da cewa kasar Sin na da yawan al’ummar Najeriya sau bakwai.
Sai dai a wani martani na gaggawa, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya ce wakilai 1,411 na Najeriya a taron COP28 da ke gudana a Dubai ba duk gwamnati ce ta dauki nauyinsu ba.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasar ya fitar a ranar Lahadi, ya ce tawagar Najeriyar ta hada da ’yan kungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa da sauran wadanda ke da mabambantan rawar da za su taka a taron.
Sai dai bai bayyana ainihin adadin wakilan da gwamnati ke daukar nauyinsu ba a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa sama da 600 na samun tallafin gwamnati ba.
Ajayi ya ce tawagar Najeriyar ta hada da shugabannin ‘yan kasuwa, masu kare muhalli, masu rajin kare yanayi da ‘yan jarida.