Jam’iyyar APC ta ce shugabanta na kasa ba ya adawa da shirin INEC na amfani da na’ura ko tura sakamakon zabe ta Internet..
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka yace Sanata Abdullahi Adamu bai taba adawa da amfani da na’ura ba wajen gudanar da zabe.
Yace shugaban APC na kasa ya nuna damuwarsa ne kawai game da kalubalen samar da wutar lantarki da kuma matsalar sadarwa.
Idan dai za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Laraba ya bayyana damuwa kan cewa Najeriya ba ta yi kwarin da zata iya amfani da na’ura da sauran fasahar zamani a zabe ba.
Yana kuma bayyana matsalar yanayin sadarwa amatsayin abunda ka iya kawo cikas.
Tuni dai babar jam’iyyar hamayya a kasar PDP ta caccaki shugaban na jam’iyyar APC kan shakku da ya nuna game da amfani da na’ura da kuma hanyoyin sadarwa wajen tura sakamakon zaben 2023 daga rumfunan zabe.
Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyya mai mulki ta tsorata akan yadda BVAS, zai iya takaita yiwuwar yin magudin zabe.