Wasu rahotanni na nuni da cewar matsalar karancin man fetir ta sake kunno kai a birnin Ikko da kewayenta, a yayin da mafi akasarin masu gidajen mai suka rufe wuraren siyar da man ga masu motoci da sauran masu amfani da shi a yau da kullum.
Koda a makon jiya an fuskanci irin wannan matsalar a Abuja da kewayenta,Matsalar da dillalan man suka alakanta da lalacewar hanyoyi da kuma tsadar da man dizal yay i, wanda da shi ake amfani jigilar man.
Da dama daga cikin manyan dillalan mai da kuma masu zaman kansu sun kauracewa kasuwancin man, a yayin da suka kyale kanfanin mai na kasa, a matsayin wanda yake bada man a jihar Legas.
Duk da daidaita harkokin tafiyar da Albarakatun man fetir da aka yi, sai dai har yanzu da dama daga cikin ‘yan kasuwar man, ba su iya shigo da man fetir din, sakamakon rashin tabbas kan samun canjin dala a bisa farashi mai rahusa, wanda yanzu haka ta haura naira dubu 1 a kasuwannin bayan fage.