Dillalan Mai sunyi korafin cewar an samu karuwar farashin man fetir da suke sayowa daga Rumbunan ajiyar mai zuwa naira 720 akan kowacce lita daya, A yayin da mafi akasarin rumbunan ajiyar man suka kasance a kulle sakamakon karancin man da ake fuskanta, biyo bayan matsalolin da suka danganci canjin kudaden kasashen waje.
Sun baiyana cewar a saboda haka ana cigaba da rufe gidajen mai da dama a kowacce rana, wanda hakan kuma zai iya haifar da matsalar karancin man fetir a yan watanni masu zuwa a fadin kasar nan.
Da yake tabbatar da korafin dillalan man, Shugaban kanfanin mai na PETROCAM Trading Nig Ltd. Patrick Ilo, Ya ce man da kanfaninsa ya sayo har tan dubu 52 a Talatar data gabata, ya saye shi ne akan naira 720 kan kowacce Lita daya, batare da biyan wani tallafin mai a cikinsa ba.
Y ace a sakamakon tashin farashin man da aka samu a halin yanzu, farashinsa zai iya kaiwa naira 729 akan kowacce Lita daya jahar Legas, idan har da gaske gwamnatin tarayya ta dena biya tallafin mai.
Ya dora alhakin tashin farashin man, da kalubale na canjin kudi, inda ya jaddada cewar har yanzu gwamnatin tarayya tana biyan tallafin mai ta bayan fage.