Kotun sauraron karrakin zaben gwamna a Jihar Kano ta karbi rubutattun bayanai na karshe daga Lauyoyin bangarorin biyu, Jam'iyyar APC da NNPP.
Kotun dake da alkalai uku Karkashin Jagorancin mai shari'a Justice Akintan Osadebay za ta ayyana ranar da za a yanke hukunci nan gaba kadan.
Bayan karbar bayyanan Kotun ta godewa dukkanin Lauyoyin bisa hadin kan da suka bayar har Shari'ar ta zo Karshe tare da alkawarin yin dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an yi hukunci cikin adalci
Zaman Kotun na wannan rana ta Litinin ya samu halattar kusoshi daga gwamnatin Jihar Kano da suka hada da sakataren gwamnati da kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki, kazali jiga jigai a Jam'iyyar APC suma sun halacci zaman Kotun.