A yankin Kudu-maso-Yamma, wasu sabbin bayanai sun na cigaba da fitowa a karshen mako kan dalilin da ya sa aka janye jami’an hukumar taro ta farin kaya DSS da ke aiki tare da gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke.
Wata kungiyar rajin farfado da jihar Osun ta nusar da batun janye jami’an na DSS a ranar Asabar a cikin wata sanarwa dauke da sahannun shugaba da sakatarenta, Saheed Bakare da LanreAkeju.
Kungiyar, ta ce rashin aiki yadda ya kamata ga jami’an shine ya sa rundunar reshen jihar Osun ta janye su.
Sai dai binciken da jaridun Punch ta yi ya nuna cewa an samu rashin jituwa tsakanin rundunar ‘yan sandan da jami’an DSS da aka tura domin yin aiki da Adeleke a ranar Alhamis din da ta gabata kan batun tura jami’an DSS daga Abuja zuwa gidan gwamnatin jihar.
Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne yayin da aka nada sabon jami’in da aka tura amatsayin babban jami’in tsaro na fadar gwamnatin daga bisani.