Kwamitin bincike mai zaman kansa na musamman na hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa ya ziyarci babban birnin jihar Adamawa, domin ci gaba da gudanar da bincike kan zargin zubar da ciki da ake yi wa sojojin Najeriya.
Kwamitin, karkashin mai shari’a Abdu Aboki mai ritaya, yana binciken zargin da ke kunshe a cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya fitar a watan Disambar 2022, cewa sojojin Najeriya na da hannu wajen zubar da ciki kimanin dubu 10 a Asirce da shirin zubar da ciki ba bisa ka’ida ba tun daga shekarar 2013 a yankin Arewa maso Gabas. .
A zaman da aka yi a Yola, Kwamandan Birgediya ta 28 Janar Meyidi Gurala, ya yi watsi da rahoton da ke alakanta sojojin Najeriya da zubar da ciki, da cin zarafin mata da 'yan mata ko kuma kashe kananan yara.
A nasa bangaren, Kwamandan Brigediya ta 23, Brig. Janar Ahmed Gambo wanda shi ma ya bayar da shaida a gaban kwamitin, ya ce a lokacin da ‘yan ta’addan ke ci gaba da kai hare-hare, sojoji ba su da alaka da farar hula, saboda galibin mutanen garuruwa da rikicin ya yi kamari ne ya sa al’ummarsu sun kauracewa gidajensu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.