Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta yaba da hukuncin kotun daukaka kara da ta yi watsi da soke zaben fidda gwanin da ya samar da Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar Apc.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a yola a wani hukunci na bai daya ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke kan Emmanuel Bwacha da Aishatu Binani a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar Apc na jihohin Taraba da Adamawa.
Kotun ta bayar da umarnin a sake mika sunayensu ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a matsayin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar Apc na jihohin biyu.
Ministar ta bayyana hakan ne a taron tattaunawa na mako-mako da tawagar sadarwar fadar shugaban kasa ta shirya a Abuja.
Tellen, wacce ta bayyana karancin mata a harkokin siyasa da sauran mukamai na shugabanci a matsayin babban koma baya ga cigaban kasarnan, ta yi kira da a dauki matakin tabbatar da kashi 50 cikin 100 na mata, tana mai cewa kashi 35 da aka saba shigarwa na mata ba sa iya aiki yadda ya kamata..