Gwamnatin jihar Kano ta fara bibiya domin ganowa tare da killace mutanen da suka kamu da cutar mashako da akafisani da Deptheria a turance a jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma bayyana cewa sama da majinyata 100 ne ke karbar magani sannan wasu sama da dubu 2 sun yi jinya kuma an sallame su.
Likita mai kula da barkewar cuttuka a jihar Kano, Dakta Abdullahi Kauranmata ya shaidawa manema labarai a karshen mako cewa an tura jami’ai zuwa lungu da sako, musamman kananan hukumomin da ke da nisa domin bibiyar halin da ake ciki.
Ya ce an samu bullar cutar ta mashako a kananan hukumomi 31 cikin 44 da ke jihar kuma gwamnatin ta kafa cibiyoyin kula da masu fama da cutar.