A bangaren kiwon lafiya kuwa, Hukumar kula da ingancin Abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta bukaci masu ruwa da tsaki dasu temaka mata wajen kawar da magungunan kashe kwari masu cutarwa a kasar nan.
Shugabar hukumar,Uwar gida Mojisola Adeyeye ce ta baiyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun kakakin hukumar Olusayo Akintola wadda aka fitar a ranar lahadi, Ta baiyana damuwar ta kan illolin dake tattare da rashin yin amfani da magungunan kashe kwarin yadda ya dace,wanda hakan ke shafar samar da lafiyayyen kayan abinci a kasar nan.
Mojisole Adeyeye ta baiyana cewar, Binciken da wata kungiya mai suna Heinrich Boll Foundation ta gabatar, Ya gano cewar kaso 40 bisa 100 na nau’ikan maganin kashe kwari da ake amfani dasu a kasar nan, an haramta yin amfani dasu a kasashen turai.
Ta baiyana cewar hukumar NAFDAC zata hada gwiwa da masu bincike da masana domin tattara bayanai da hujjoji kan matakan da ya kamata ta dauka akan irin nau’ikan maganin kashe kwarin masu cutarwa.