An zabi tsohon shugaban kungiyar injiniyoyi ta kasa Mustapha Shehu a matsayin sabon shugaban kungiyar injiniyoyi ta Duniya.
Wannan abun tarihi ya faru a babban taron kungiyar na duniya dake gudana yanzu haka a San Jose na kasar Costa Rica.
Mustapha Shehu wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar injiniyoyi ta kasa, ya samu nasarar darewa kan kujerar ne bayan samun kuri’a 67 daga cikin 71 da aka kada, wanda hakan ya bashi damar hawa kan matsayin.
A wata sanarwa da kungiyar injiniyoyi ta duniya ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta taya Mustapha Shehu murnar nasarar zama shugaban kungiyar da yay i.