Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano karkashin mai shari’a S.A Amobeda ta yankewa wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Muhammad Sambo daurin shekara 10 a gidan gyaran hali.
Sambo na daga cikin masu safarar miyagun kwayoyi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano ta kama a cikin watan Octoban da muke ciki.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Maigatari ya fiyar a ranar Litinin, ta ce bayan gurfanar da wanda ake tuhumar gaban kotun, an yanke masa hukuncin daurin shekara 10.
Sanarwar ta baiyana cewar kwamandan hukumar Abubakar Ahmad ne ya jagoranci gurfanar da wanda aka yanke hukuncin gaban kotu.