Rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasa, Peace corps reshen jihar Kano, ta yabawa majalisar wakilai ta kasa bisa amincewa da kudirin dokar kafa rundunar, wanda a yanzu haka yake gaban majalisar dattawa domin samun amincewarta kafin tura shi wajen shugaban kasa don saka ma dokar hannu.
Babban kwamandan rundunar reshen jihar kano, Musbahu Ado Ibrahim CGPM ne ya yi wannan yabo, ya ce matakin da majalisar wakilan ta dauka abun a yaba mata ne, la’akari da irin yadda aka jima ana kishirwar ganin kafuwar rundunar ta tabbata.
Musbahu Ado Ibrahim CGPM y ace makasudin kafa rundunar shi ne domin wanzar da lafiya a tsakanin yan kasa tare da dafawa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan kasa das u rika temakawa hukumomin tsaro da bayanan kan duk wani bakon abu da basu amince da shi ba.