Babban layin wutar lantarki na kasa karkashin kulawar kamfanin tura wutan lantarki na kasa TCN ya lalace da tsakar daren yau Alhamis, al'amarin da ya jefa Najeriya cikin duhu baki ɗaya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa durkushewar na zuwa ne makonni kadan bayan da kamfanin tura wutar lantarki na kasa TCN ya yi bikin shafe sama da shekara guda ba tare da samun durƙushewar wutar lantarki a Najeriya ba.
Wata sanarwar da kamfanin Rarraba Lantarki na Enugu (EEDC) ya fitar, ya ce ɗurƙushewar ta afku ne da karfe 12:40 dare s wanda ya yi sanadin daukewar wuta a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta ce saboda wannan matsala ta durƙushewar layin wutar lantarki a Nageriya, duk tashoshin TCN ba su da wadatar turawa abokan hulda hakan yasa ba za'a iya tura wuta ga jihohin Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo ba.