Wasu kungiyoyin farar hula sun yi All..h wadai da tsabar kudin da aka ware a cikin kunshin kasafin kudi har Naira biliyan 30 da milyan dari matsayin kudin sallama ga ‘yan majalisar dokoki ta kasa da kuma kaddamar da sabon zauren majalisa mai zuwa
A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar dokoki ta kasa ta kara kudurin kasafin kudin shekarar 2023 daga Naira tiriliyan 20 da bilyan 51 zuwa Naira Tiriliyan 21 da bilyan 82, sannan ta amince da shi, wanda hakan ya nuna karin sama da Naira Tiriliyan 1 da bilyan 300 akan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a watan Oktoba.
Da yake tsokaci kan lamarin, Shugaban kungiyar dake saka ido kan aiyukan yan majalisa da kuma bada shawarwari ta CISLAC, Auwal Rafsanjani, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda majalisar kasa ta yi kasafin kudin da bai da wata alaka da jama’a, Yana mai cewa tsarin anyi shine kawai a salon nan na kashin dankali.