On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Umarci Masu Mitocin Lantarki Su Sabunta Mitocinsu Kafin Watan Nuwambar 2024

MITA

Hukumar Sadarwa ta kasa, NCC, ta bayyana cewa masana'antun cikin gida sun samu kudaden shiga da ya haura Naira bilyan 55 sakamakon hana shigo da Layukan waya cikin kasar nan.

Idan za a iya tunawa, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani,  Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a yayin  wani  bikin baje kolin kayayyakin sadarwa da aka gudanar a shekarar da ta gabata, ya sanar da hana shigo da layukan waya cikin kasar nan.

Da yake tsokaci  kan  irin nasarorin da hukumar ta samu wajen inganta abubuwan da suka shafi cikin  gida,  Shugaban hukumar  sadarwa  ta kasa  Farfesa Umar Garba Danbatta, ya ce   hana shigo da layukan waya daga kasashen waje, ya temaka wajen saukaka bukatar  samun kudin kasashen waje a kasar nan.

Ya kara da cewa haramcin ya temakawa  yan kasuwar  gida  masu kera  Layin waya  da kansu wajen samun kudin shiga  har   Naira biliyan 55 .