Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro da za su bada kulawa da matafiya a titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, yayin da a yau litinin ake dawowa cigaba da jigilar Fasinjoji bayan kusan wata tara da dakatarwa sanadiyar harin ‘yan ta’adda.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako, ya ce za a zabo jami’an ne daga wata rundunar ‘yan sanda da ake kira K-9 da ofishin leken asiri na rundunar ‘yan sandan da sashen kwance abubuwan fashewa da sauran makamantansu.
Adejobi ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya na tattaunawa akai-akai da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa da sauran jami’an tsaro a shirye-shiryen dawowa aiki a yau.
Ya ce babban Sifetan ya baiwa jama’a, musamman ma fasinjoji tabbacin kulawa da rayuka da dukiyoyinsu.