An samu wani Yaro Dan shekara 14 a duniya da ke unguwar Hotoro dake nan jihar Kano, wanda iyayensa suka sanar da bacewarsa a cikin watan Maris din bana, a kasar Togo.
Rahotanni sun baiyana cewar anga yaron tare da wani karamin yaro wanda shima ya fito daga Najeriya,Suna yin bara akan Titi a can kasar ta Togo,inda suke neman Abinci.
Majiyar ta baiyana cewar an samu yaran wajen wata ‘yar Najeriya da ta yi shuhura wajen siyar da Abinci a kasar Togo mai suna Hajiya Maijidda Mai Abinci, wanda wasu mutane suka kai mata yaran, Kasance sunce su ‘Yan Najeriya ne.
Matar ta baiyanar cewar a halin yanzu ita take kula dasu, a yayin da tasa ake neman iyayensu a nan Najeriya.
Hajiya mai Abinci, ta baiyana cewar yaran sun fada mata cewar wata mata ce ta yi awon gaba dasu daga nan Najeriya zuwa kasar Ghana, inda suka yi ta rokonta data temaka ta sake su, Kafin daga bisani su tsinci kansu a kasar ta Togo.
Mahaifin yaron , Ya godewa hajiya mai Abinci saboda kishin data nuna, Tare da rokon Al’umma su temaka masa,Kasancewar bashi da kudin da zai biya domin dawo da yaron nasa gida Hotoro dake nan Kano.