Gwamnatin Turkiyya ta tsare wasu 'yan kwangilar gine-gine sama da 100 biyo bayan girgizar kasar da tayi ajalin mutane sama da dubu 33 a kasar.
Ma'aikatar shari'ar kasar ta ware wani sashe na musamman na bincike da zai binciki 'yan kwangilar gine-gine, wadanda gine-ginensu suka rushe a lokacin girgizar kasar, inda dubban 'yan kasar Turkiyya suka mutu.
Yanzu haka sashin binciken ya tsare sama da ’yan kwangilar gine-gine 100, wadanda watakila ke da alhakin rushewar gine-gine saboda zargin rashin cika ka’idojin gini.
An kama daya daga cikin 'yan kwangilar da ke da alhakin wani katafaren gidaje na alfarma da suka ruguje a lardin Hatay a filin jirgin sama yayin da suke kokarin tserewa daga kasar.