On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Tashi Baran-Baran A Shari'ar Sheik Abduljabbar

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara a zaman kotun yau

Lauyan Abduljabbar ya kwashe Komatsansa tare da ficewa daga cikin kotu, bayan da ya zargi Alkali da marawa gwamnatin Kano Baya.

Antashi baran-baran a cigaba da shari'ar Abduljabar Nasiru kabara da gwamnatin Kano kan zargin Kalaman batanci ga annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasalam.

Inda a yau lauyan abdujarbar Barista Dalhatu Shehu Usman ya roki kotun da ayi hukunci kan sallamar sheik abdujarbar kamar yadda suka nema a baya, inda  mai shari'a Ibrahim Sarki yola yayi  alkawari tun a zama na baya,  sai dai a yau mai shari'a yace sai a karshen shari'ar zai baiyana matsayar kotu.

Jin haka lauyan Abdujarbar Barista Dallahatu ya kwashe kayansa daga kotu, Sannan Kuma ya fice daga kotun, inda ya zargi kotu da goyan bayan gwamnati da kuma rashin adalci a cikin shari'ar, Sannan Kuma yace  zasu tafi kotu ta gaba.

Sai dai tsagin lauyoyin gwamnati sun baiyana abunda lauyan yayi, a matsayin raina kotu.

Kamar yadda wakilinmu Ado Danladi Farin Gida ya habarto mana daga kotun.