An tashi batare da cimma wata matsaya ba a ganawar da aka yi tsakanin Gamaiyyar kungiyoyin kwadago na kasar nan, da kuma wakilan gwamnatin taraiyya kan batun cire tallafin mai, a daren jiya.
Ganawar dai ta biyo bayan sanarwar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ta cewar an kawo karshen maganar biyan tallafin mai a kasar nan, da kuma sabon farashin litar man fetir da kanfanin mai na kasa ya sanar a jiya.
Da yake jawabi jim kadan bayan tashi daga ganawar, Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Kwamared Joe Ajaero, ya ce za’a cigaba da tattaunawar, kasancewar babu wata masalaha da aka cimmawa a yayin zaman nasu da wakilan gwamnatin taraiyya.
Kazalika ya koka kan yadda kanfanin mai na kasa ya sake kara farashin man fetir kafin ganawar da suka yi a daren jiya.
Shima da yake nasa jawabin a madadin gwamnatin taraiyya, Daraktan yakin neman zaben Tinubu da Shettima, Dele Alake, Ya ce za’a cigaba da tattaunawa a tsakaninsu domin samo mafita akan matsalolin.