Majalisar koli kan harkokin shari'a ta kasa NJC ta bada shawarar anada alkalai 11 amatsayin Alkalan kotun koli.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na majalissar, Soji Oye ya fitar a ranar Laraba, ta ce an cimma matsayar ne a karshen zaman majalisar na 104.
Kundin tsarin mulkin kasarnan ya tanadi alkalai 21 a kotun koli amma a halin yanzu kotun tana da alkalai 10 mafi karanci a tarihi.
Hukumar NJC ta tantance ‘yan takarar zama Alkalan kotun koli 22 da hukumar kula da harkokin shari’a ta tarayya ta tantance, kuma a ranar Laraba ta zabi sunayen mutum 11 da suka yi nasara a shafinta na intanet.
Ana sa ran hukumar ta NJC za ta mika sunayen ga shugaban kasa domin amincewa da su kafin ranar Juma’a.