Gwamnatin jihar Legas ta ce an tabbatar da cewa dabbobi shida a jihar suna dauke da cutar anthrax.
Ma’aikatar noma ta jihar ta bakin babban sakatarenta, Olatokunbo Emokpae, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya ce an gano cutar a tsibirin Legas da Agege.
Emokpae ya ce an kwace dabbobin an kona su tare da binne su, don hana yaduwar cutar, ya kara da cewa ba a samu rahoton kamuwa da cutar a jikin dan adam ba tun bayan da aka samu cutar a jihar.
Anthrax kamuwa da cuta ce mai yaduwa amma Yawanci tana shafar dabbobin kamar shanu da tumaki, da kuma awaki.