A yaune Majalisar Dokokin jihar Kogi ta sauke wasu Shugabanninta 4 tare da Dakatar da wasu 3 bisa samunsu da aikata lefin rashin Da’a.
Yan Majalisar sun dauki wanan mataki ne a yayin wani zaman gaggawa da suka yi a harabar zauren maajlsiar, biyo bayan wani kudurin gaggawa da Dan Majalisa Enema Paul na jam’iyyar APC ya gabatar.
Shugabannin Majalisar da aka dauki matakin saukewar a kansu, sun hada da Ahmed Mohammed wanda ya kasance Mataimakin kakakin Majalisar da bello Hassan Abdullahi shugaban Masu Rinjaye sai Ndako Idris Mataimakin Shugaban Masu rinjaye da kuma Mister Edoko Ododo mataimakin Bulaliyar Majalisar.
Kazalika daga bisani yan Majalisa 17 da suka dauki matakin, sun maye gurbin wadanda suka sauke da Rabiu Alfa a matsayin Mataimakin Kakaki sai Bajeh Muktar Shugaban Masu Rinjaye da umar Isa Mataimakin Shugaban Masu rinjaye da kuma Enema Paul mataimakin Bulaliyar Majalisar.