Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta umarci shugaban Asibitin kula da masu larurar Mafitsara na Abubakar Imam Dr Atiku Adamu da kuma shugaban Likitoci na Asibitin Dr Kabiru Ahmad, dasu sauka daga kan matsayinsu a nan take, har zuwa lokacin da za’a kamma gudanar da bincike bisa zarginsu da aikata almundahanar kudi.
An dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da aka samu wanda suka da karbar kudi daga hannun marassa lafiya, da tura marassa lafiya zuwa asibitoci masu zaman kansu domin yi masu magani ko kuma tiyata, da kuma zargin aikata lefin almubazzaranci.
Wata sanarwa mai dauke dasa hannun jami’ar hulda da jama’a ta Hukumar, Samira Suleiman, Ta ce shugaban hukumar, Dr Mansur Mudi Nagoda ne ya bada umarnin, bayan amincewa da daukar matakin da kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya yi.
Sanarwar ta kuma baiyana cewar hukumar ta amince da yin sauyin wurin aiki ga daukacin ma’aikata da masu tarbar marassa lafiya zuwa wasu asibitocin, tare da maye gurbinsu da wasu batare da bata loakci ba.