On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

An Sanya Dokar Hana Fita A Jihar Kano Sa'oi 24 Domin Tabbatar Da Doka Da Oda.

Gwamnatin Jihar Kano ta hannun rundunar 'yan sanda ta ayyana dokar hana fita sa'oi 24 domin tabbatar da doka da oda.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun  rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta tsara dabaru tabbatar da tsaro a cikin gida  tare da yin kira ga al’umma  su bada goyon baya da ake bukata. 

Yace matakin yunkurin ne na sauke nauyin  kundin tsarin mulkin Najeriya da ya dorawa  rundunar da da jami’an tsaro na cikin gida na tabbatar da  doka da oda.

Sanarwar ta yi kira ga  al’ummar Jihar Kano su kasance masu biyayya ga doka yayinda aka aike da jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa lungu da sako domin tabbatar da aiwatar da  bin dokar hana fita ta sa’o’i 24.

Kiyawa ya ce, gwamnatin Jiha ta sanar da rundunar bukatar daukar matakin sanya dokar a cikin wasika mai lamba: K/SEC/H/435/T.1/153 mai kwanan wata 20 ga Satumba, 2023 wadda zata fara aiki daga karfe 6 na yammacin yau Laraba, 20 ga Satumba zuwa karfe 6 na yammacin Alhamis, 21 ga Satumba, 2023. 

Sanarwar ta mika godiyata ga daukacin al’ummar jihar Kano masu son zaman lafiya tare da kira gare su da su ci gaba da bin doka da oda.