Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta tabbatar da karin wasu mutane 42 da suka kamu da cutar COVID-19 a cikin kasarnan cikin makonni biyu, inda jihar Legas ta samu karin mutane 27.
Hukumar NCDC ta bayyana haka ta cikin wani sako da aka wallafa a shafinta a karshen mako, inda ta kara da cewa an samu adadin mutanen a jahohin Edo da Kano da Nasarawa da Kaduna da Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar tace sabbin alkaluman sun kawo adadin wadanda suka kamu da cutar ta Corona a kasarnan zuwa dubu dari 2 da 66 da 492.
An samu sabbin mutanen ne tsakanin 31 ga Disamba na shekarar 2022 zuwa 13 ga watan Janairu da muke ciki na 2023.
A cewar rahoton, NCDC ta tabbatar da cewa Najeriya ta samu sabbin mutane 29 daga ranar 7 zuwa 13 ga watan Janairu.
Sabbin mutanen sun fito ne daga Legas da aka samu 15 sai 5 a Abuja da 4 a Kano da 3 a Nasarawa da 1 a Nasara sai 1 a Plateau.
Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa na ci gaba da bayar da shawara ga ‘yan Najeriya su karbi rigakafin COVID-19.