On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Samu Rabuwar Kawuna Tsakanin Shugabannin Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa Ta Kasa

LIKITOCI NA ZANGA-ZANGA

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa, ta dage taron kwamitin kolinta data shirya gudanarwa har sai zuwa ranar Laraba.

Ana saran  kwamitin kolin kungiyar zai dauki mataki akan  yuyuwar  tafiya yajin aiki ko kuma akasin haka, bayan wa’adin makwanni biyu da suka bawa gwamnatin taraiyya  domin biya masu bukatunsu ya cika, amma batare da samun biyan bukata ba.

Rahotanni na baiyana cewa an so gudanar da taron ne a ranar  Asabar  amma hakan bai yuba, a sakamakon rarrabuwar  kawunan da aka samu a tsakanin ‘yan kwamitin gudanarwar kungiyar na kasa.

A zantawarsa da manema Labarai a ranar  Lahadi, Shugaban Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta kasa Dr Dare Ishaya, Yace  kungiyar ta dage  taron  zuwa  ranar Laraba, kuma zata yi shi ne kai tsaye  ta hanyar amfani da Allon gani gaka.