Najeriya ta samu wani gagarumin cigaba ta bangaren amfani da hanyoyin sadarwa a cikin watanni bakwai da suka gabata daga watan Nuwamba 2021, inda aka samu sabbin mutane har miliyan bakwai da suka fara yin amfani da internet, wanda hakan ke nuna ci gaban da aka samu ya cimma kashi 70 cikin 100 da ake son cimmawa nan da shekarar 2025.
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya Farfesa Umar Danbatta, wanda ya baiyana alkaluman a cikin wata sanarwa, ya ce ci gaban da ake samu a hanyoyin sadarwa na internet yana matukar tasiri ga sauran bangarorin tattalin arziki kamar kiwon lafiya, ilimi da noma sai harkokin kudi da sufuri da kasuwanci da mulki da kuma sauran wasu sassa.
A yanzu haka dai Masu amfani da Intanet sun karu daga miliyan 90 a shekarar 2015 zuwa miliyan 150 da dubu 36 kamar yadda kididiga ta nuna a watan Mayun 2022.
Daga karshe, Ya yabawa al’ummar kasar nan, bisa ga irin cikakken goyon bayan da suke bawa hukumar a kowance lokaci wanda haka yasa take samun nasarori masu yawan gaske, Sannan kuma yace hukumar zata cigaba da bijiro da sabbin tsare-tsare da zasu inganta bangaren.