Hukumar aikin hajji ta kasa ta ce kimanin Alhazai mata masu daukar da juna biyu 75 ne aka kwantar a wasu Asibitoci dake birnin Makkah da kuma Madina domin samun kulawar gaggawa.
Shugaban tawagar likitoci na hukumar aikin hajji ta kasa, Usman Galadima ne ya baiyana haka, Ya ce duk da fadakarwar da suka rika yi akan kauracewa zuwa aikin hajji ga mata masu dauke da juna biyu, amma an samu wasu da suka yi wa fadakarwar kunnen kashi.
Ya kuma baiyana cewar tawagar likitocin na fama da larurori da maniyyatan suka fi fama dasu kamar ciwon siga da hawan jini.
Kazalika ya baiyana cewar asibitin sha ka tafi na hukumar aikin hajji ta kasa dake saudiyya na samun karuwar alhazan da ke fama da rashin lafiya.