Rahotanni na baiyana cewa Yan ta’adda sun sako ragowar fasinjojin jirgin kasar da suka sace a ranar 28 ga watan Maris din bana.
Farfesa Yusuf Usman ne ya tabbatar da hakan a madadin gwamnatin taraiyya ta cikin wata sanarwa da ya fitar , inda ya baiyana cewa an sako mutanen ne da kimanin karfe 4 na yammaci.
Idan ba’a manta ba, yan ta’addar da suka kaiwa jirgin hari a kaduna sun rika sakin fasinjojin rukuni zuwa rukuni , wanda kuma kason karshe da suka saki sune na ranar 19 ga waan Augustan Bana.
Kazalika an kama wanda ke shiga tsakani mai suna Tukur Mamu a ranar 6 ga watan jiya a birnin Alkahira na kasar Masar a kan hanyarsa a zuwa Saudiya, inda aka damkashi hannun Hukumar tsaro ta DSS, wanda ta zarga da tallafawa yan ta’adda.