On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Saki Tsohon Shugaban EFCC Bawa Bayan Shafe Sama Da Kwanaki 100 A Tsare

Bayan shafe sama da kwanaki 100 a tsare, an saki tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Abdurasheed Bawa.

Idan za’a iya tunawa hukumar DSS ta kama Bawa ne a ranar 14 ga watan Yuni na  2023, sa’o’i bayan dakatar da shi daga mukaminsa na shugaban Hukumar EFCC da Shugaba Bola Tinubu ya yi kan wasu zarge-zarge.
An sako Bawa ne a daren Laraba a Abuja. 
DSSS ba ta fito fili ta shigar da kara  ba ko kuma bayyana irin laifin da ya aikata tun bayan kama shi da tsare shi.
Mai magana da yawun hukumar DSS  Peter Afunanya, yace an saki Bawa a ranar Laraba. 
Wani  video ya karade kafafen sada zumunta inda aka ga Matan Bawa da yaransa na yi masa maraba da komawa gida.