’Yan ta’addan sun sako mutum shida ’yan gida daya daga cikin fasinojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ke hannunsu.
Daily trust ta gano cewa an sako iyalan ne bayan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shiga tsakani.
Mawallafin Jaridar Desert Herald da ke Kaduna, Tukur Mamu, ya ce Gumi ne ya shiga tsakani bayan ya tattauna da ’yan ta’addan a karon farko tun bayan faruwar lamarin a ranar 28 ga watan Maris, 2022.
“Ya roke su da su sako kananan yaran da iyayensu da ba su ji ba, ba su gani ba; An gano cewa yanayin lafiyar biyu daga yaran ya tabarbare tun bayan bulalar da ’yan ta’addar ya wa shafi mahaifinsu,” inji shi.
Mahaifin yaran hudu ma’aikaci ne na Hukumar Majalisar Dokoki ta Kasa, amma dai babu wani shiga tsakani da Hukumar ko Majalisar ta yi tun lokacin da abin ya faru.
(Karin magana:..Ba'a fafe gora ranar tafiyar)