Ana fargabar mutane da dama sun mutu a karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, a ranar Litinin, yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife.
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Dr. Mohammed Suleiman, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce ya faru ne da rana kuma ana ci gaba da aikin ceto.
Wannan Iftila’I na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da mutane takwas suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Yola ta Kudu, yayinda akalla mutane 24 suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a jihar Neja ranar Lahadi.
Mahmud, wani masunci a yankin da ke cikin masu aikin ceto, ya shaidawa manema labarai cewa, za a iya hana aukuwar al’amarin idan fasinjojin sun yi amfani da rigar kariya tare da aiwatar da wasu matakai na kariya.