An kammala Ganawar da aka sake yi tsakanin wakilan gwamnatin taraiyya da Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU batare da cimma wata matsaya ba.
Dukkanin wani fata na ganin an warware matsalolin da suka haddasa tafiya dogon yajin aiki da malaman jami’oin keyi, a zaman da suka yi da kwamitin da gwamnatin taraiyya ta kafa a karkashin Farfesa Nimi Brigss, a zaman da suka yi a jami’ar Kasa dake Abuja, ya karkare batare da samun bakin zaren ba.
Wani mamba a cikin kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Wanda ya nemi manema Labarai su sakaye sunansa, Yace kwamitin farfesa Brigs bai zo masu da wani sabon tayi ba a yayin zaman da suka kwashe tsawon sa’oi ukku suna yi a tsakaninsu.
Yace kwamitin ya roki Malaman ne kawai dasu janyen yajin aikin da suke yi , bisa alkawarin cewa za’a shigar da dukkanin bukatunsu a cikin kunshin kasafin kudi na shekara mai zuwa.