A wani bangaren kuma, Hukumar Yaki da Cin hanci da karbar Rashawa ta sake bankado wat naira milyan 258 da aka boye a wani banki, a yayin da ake tsaka da fama da matsalar rashin kudi a hannu a kasar nan.
Kakakin hukumar, Azuka Ogugua ya ce kudin da jami’an hukumar suka gano sabbi ne baki dayansu , Inda aka samu kudin a cikin bankin Sterling.
Ya kara da cewa Babban bankin kasa ne ya saki kudin domin a rarraba su ga abokan huldar bankuna, amma bankin ya boye su.
Hakan na zuwa ne kasa da kwana daya bayan da Manajan wani banki ya fada komar hukumar EFCC a Abuja bisa zarginsa da kin raba sabbin kudi har naira milyan 29 ga abokan huldar bankin.