On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Sake Dakatar Da Likita A Jihar Kano Saboda Kauracewa Bakin Aiki

Shugaban hukumar kula da asibitoci a jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya sake dakatar da wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Ana zargin likitan ya bar aikin sa ne tsawon dare daya a ranar Litinin.

Dr Nagoda wanda ya kai ziyarar bazata da karfe 12 na dare kuma ya tafi da  karfe 5 na Asuba, ya tarar da rashin likita a bakin aiki kuma bai iya samunsa ko a waya ba.

Shugaban kula da asibitocin ya koka da cewa bayan dakatarwar da aka yi wa wasu likitoci a ranar Litinin, yanasa ran cewa duk sauran likitoci da ma’aikatan jinya da ke wasu cibiyoyin lafiya zasu dauki ayyukansu da muhimmanci.

Idan dai za a iya tunawa a baya hukumar ta sauke shugabannin wasu asibitoci uku a jihar Kano inda ma’aikatan lafiya suka kauracewa ayyukansu a  daren ranar 30 ga watan Yuli da ya gabata.