On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Saka Dokar Hana Fita A Jihar Gombe Saboda Kisan Gillar Da Aka Yiwa Wani Malami

GOMBE

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanya dokar hana fita daga Karfe 12 na tsakar dare zuwa karfe 6 na safe, a wani mataki data dauka biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Albani

A ranar Laraba ne aka   halaka  Sheikh Ibrahim Musa Albani  a gidansa  dake  Gombe.

Majiyar ‘yan uwansa  ta ce wasu mutane hudu dauke da adduna rufe fuskokinsu sun farwa  malamin addinin musuluncin tare da halaka shi har  lahira  a  gidansa da ke unguwar Tabra a   jihar  Gombe da misalin karfe 3 na   dare.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Oqua Etim ne ya bayar da umarnin saka  dokar  hana  fitar  kamar  yadda  yake  cikin  wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar  ASP Mahid Abubakar ya fitar.

Duk  da cewar  Dokar hana fitar  zata hana  mutane samun sukuni  kamar  yadda  rundunar  ta baiyana, Sai dai ta  ce   dokar  na  da nufin kiyaye lafiyar jama’a, da dakile yawaitar ayyukan ta’addanci, da kuma tabbatar da doka da oda a fadin jihar.