On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Sace Tsabar Kudi Naira Milliyan 31 A Gidan Gwamnatin Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da rahotannin sace miliyoyin naira da wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi a sashin ajiyar kudi na fadar gwamnatin jihar.

Babban daraktan gwamnan kan sabbin kafafen yada labarai, Alhaji Al-Amin Isah, ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.

Ko da yake Isah bai iya bayyana adadin kudaden da aka sace ba, ya ce tuni wasu daga cikin wadanda ake zargi suka shiga  hannun ‘yan sanda kuma ana  gudanar da bincike.

Sai dai wasu majiyoyin da ke da masaniya kan al’amarin sun yi nuni da cewa, kudaden da aka sace sun kai Naira miliyan 31.

Wannan dai shi ne karo na biyu da irin wannan al’amari ke faruwa a Katsina.

A watan Janairun 2020, irin wannan al’amari ya faru lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kutsa cikin ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa, tare da yin awon gaba da Naira miliyan 16.