Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace kwamishinan yada labarai da raya al’adu da kuma yawon bude ido na jihar Yakubu Lawal, da wasu ‘yan bindiga suka yi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa DSP Ramhan Nansel shine ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a safiyar yau a Lafia babban birnin jihar.
Ya ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun yi awon gaba da kwamishinan yada labaran, bayan da suka kai farmaki gidansa.
Ya kara da cewa a yanzu haka ana gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakaninsu da jami’an tsaro baturen yansandan Akwanga, ACP Halliru Aliyu domin ganin an kubutar da kwamishinan cikin salama sannan kuma a kama wadanda suka aikata lefin.