Gwamnatin jihar Borno ta ce ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira hudu tare da sake tsugunar da ‘Yan gudun Hijirar a wasu gidaje Dubu 11 data samar a wasu yankuna shida dake jihar.
Gwamna Babagana Zulum wanda ya yi jawabi a yayin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira hudu a ranar Alhamis a birnin Maiduguri, ya ce an samu nasarar hakan ne biyo bayan dawowar zaman lafiya a jihar.
Gwamnan yace sansanonin ‘yan gudun hijirar da aka rufe sun hada Dalori ta Daya sai Dalori ta 2 da sansanin ‘yan gudun hijira dake kan hanyar zuwa Gubio da Muna El-Badawi, inda ya ce a shekarar 2015 ne, mayakan Boko Haram suka raba mutanen da muhallansu.
Gwamnan ya danganta rufe sansanonin da matsalar karancin kudade, inda ya kara da cewa a yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin rufe wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar tare da mayar da mutanen garuruwansu na asali na da shekara ta 2023.