Hukumomin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi sun rufe makarantar na tsawon mako guda bayan wata zanga-zangar da dalibai suka gudanar ranar Litinin.
'Daliban sun yi zanga-zangar ne bayan kisan wani dalibi mai suna Joseph Agabaidu, dalibi dan aji 5 na sashen nazarin kasa na tsangayar kimiyya, da wasu mahara dauke da makami suka yi.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ATBU Bauchi Zailani Bappah ne ya bayyana haka ga manema labarai a Bauchi.
Bappah ya tabbatar da mutuwar dalibin kuma ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka cakawa marigayin Agabaidu wuka a kokarinsu na kwace wayarsa, sai dai yace al’amarin bai faru a harabar makarantar ba amma a wajen makarantar ne kuma hakkin ‘yan sanda ne su binciki al’amarin.