Hukumar kula da shige da fice ta kasa ta ceto wasu mutane takwas da ake yunkurin safararsu a jihar Jigawa.
Kwanturolan hukumar reshen jihar Jigawa, Ahmad Dauda Bagari shine ya tabbatar wa manema labarai hakan ofishinsa dake Dutse babban birnin jihar.
Ya ce jami’an hukumar ne suka kama wadanda al’amarin ya rutsa da su a ranar Lahadi a kan hanyarsu ta tsallakawa Jamhuriyar Nijar a karamar hukumar Roni.
Wadanda aka kubutar sun hada da maza biyar da mata uku daga jihohi hudu na Abia da Edo da Imo da kuma Ogun, kuma shekarunsu na tsakanin 19 zuwa 45, ba su da ingantattun takaddun balaguro.
Bagari, Yace mutanen suna tafiya ba tare da wakili ba, inda suke yin duk ma'amalarsu ta waya, sai dai ya nunar da cewa babu wani abu da aka samu na laifi ko kwaya a hannunsu.
An bada umarnin mika mutanen ga hukumar NAPTIP sannan kuma ya shawarci iyaye da ‘yan uwa da sauran jama’a da su daina yarda suna tura ‘ya’yansu zuwa kasashen waje kasancewar Najeriya tana da yanayi mai kyau na rayuwa mai inganci tare da sanya kishin kasarsu ta asali da kuma gina ta zuwa ga kololuwar mataki.
Haka kuma hukumar ta kara shawartar jama’a da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar kai rahoton laifukan safarar mutane da sauran laifuffuka masu alaka da su ga hukumomin tsaro mafi kusa.