Hukumar shige da fice ta kasa ta baiyana cewar,Jami’anta kimanin 80 ne suka fuskanci shari’a gaban kotu saboda karbar Na goro, a lokacin da suke bada fasfo ko sabunta shi ga masu bukata.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Tony Akuneme, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Lahadi, Ya kuma ce an kori wasu guda takwas saboda samunsu da aikata lefuka daban daban a shekarar data gabata.
Ya kara da cewar matakan ladabtawar da hukumar ke dauka,wani bangare ne na kokarin kawo gyara da sauye-sauye a hukumar shige da fice ta kasa, karkashin mukaddashin shugaban hukumar Isah Jere.
Bugu da kari ya ce, Shugaban hukumar ya ci alwashin hukunta duk wani jami’in shige da fice da aka samu da yunkurin yiwa aiyukan hukumar zagon kasa.