Gwamnatin jihar Edo ta kori malamai 13 na jami’ar Ambrose Ali daga bakin aiki, bisa laifukan da suka hada da karyar shekaru da zamba da rashin ‘Da’a da cin zarafi da kuma musgunawa dalibai.
Shugaban jami’ar, Farfesa Asomwan Sunny Adagbonyin, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa na jami’ar ga mambobin tawaga ta musamman.
Ya ce korar ma’aikatan ya biyo bayan shawarwarin kwamitin ladabtarwa da ya same su da aikata laifukan.
An bada shawarar korar daya daga cikin malaman da ke shugabantar sashen ilimin aikin jinya daga aiki bayan da rahotanni suka ce an same shi da laifin karbar kudi naira dubu 32 da dubu 52 daga hannun dalibai.