Sufeton Rundunar ‘Yansanda ta kasa, Usman Alkali Baba Ya karrama Baturen ‘Yansanda na Karamar Hukumar Nasarawa dake nan jihar Kano, SP Daniel Itse Amah, sakamakon yadda yaki karbar cin Hancin Dala Dubu 200 da aka yi yunkurin bashi kan wata tuhuma ta zargin aikata lefin fashi da Makami.
An bawa baturen Yansandan Takardar shaidar Karramawa ta musamman daga hannun sufeton yansandan na kasa, Rahotanni sun baiyana cewa zargin aikata lefin fashi da makamin ya shafi wani Lauya ne da kuma wasu jami’an ‘yansanda.
Ta cikin wata wasikar yabo, An jinjinawa mister Amah bisa yayi amfani da kwarewarsa wajen jagorantar cafke Lauyan mai suna Ali Zaki da kuma wasu Jami’an ‘yansanda.
Tuni dai aka mika tuhumar zuwa ga shalkwatar rundunar yansanda ta kasa dake Abuja, sakamakon umarnin da sufeton yansanda na kasa ya bayar, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yansanda ta kasa Olomuyiwa Adejobi ya baiyana.