Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zargi da sayan kuri’a a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi
Wata sanarwa da kakakin hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ta fitar, ta bayyana cewa an kama wani mai suna Dapo Oloyede a karamar hukumar Ife ta Arewa, yayin da aka cafke wani mai suna ‘Kamorudeen Nafisat da Ojuade Olaniyi a karamar hukumar Egbedore.
A cewar sanarwar, an kama daya daga cikin masu siyan kuri’a dauke da jerin sunayen mutane 100 da ke sa ran za a biya su Naira dubu 5000 kowannensu.