Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta kama tare da tsare, Injiniya Idris Wada Saleh kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, da wasu mutane biyar bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Saleh, wanda kuma shi ne tsohon shugaban hukumar kula da gyaran Tituna Kano a ranar Litinin da yamma tare da babban sakatare na ofishin kula da bada kwangilolin gwamnati, Mustapha Madaki da Daraktan kudi da daraktan bincike da tsare-tsare tare da wasu sauran mutane.
An kama su ne bisa zargin fitar da sama da Naira biliyan 1 domin gyaran tituna 30 da magudanar ruwa a cikin birnin Kano da ba a aiwatar ayyukan ba.
Wata majiya a hukumar ta yi nuni da cewa an biya kudaden da aka kashi uku ne a asusun kamfanoni uku a ranar 25 ga watan Afrilu na 2023.
Kakakin hukumar Abba Kabir ya ce wadanda aka kama suna fuskantar tambayoyi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.