An cafke wasu mutane hudu da ake zargin mayakan Boko Haram ne a birnin Yola na jihar Adamawa, lokacin da suke yunkurin kai harin Bam gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar dake birnin na Yola.
Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Jibrila Mohammed mai shekara 29 a duniya,wanda ya tabbatar da cewar shi Dan Boko Haram ne, an kama shi ne a kofar shiga gidan Atiku Abubakar, lokacin da yake kokarin kai harin da kimanin karfe 9 na daren shekaran jiya.
Sanarwar da ofishin yada labaran jam’iyyar PDP ya fitar, Ta baiyana cewar bayan kama matashin,an kuma sake damke wasu mutane ukku da suke tare dashi.
Sanarwar ta baiyana cewar an mika mutanen da ake zargi hannun sojoji,sannan kuma sun fadawa jami’an yansanda cewar, maharani sun yi niyyar kai kan wasu kungiyoyi dake aiki da Atiku Abubakar da kuma wasu muhimman wurare a birnin na Yola.