![](https://mmo.aiircdn.com/370/6398313e7e097.jpg)
'Yan sandan Bahamas sun kama Sam Bankman-Fried, mutumin da ya kafa kamfanin hada-hadar kirifto amma jarinsa ya karye wato FTX, in ji atoni janar na ƙasar
Bahamas ta ce ta karɓi sanarwa a hukumance daga Amurka kan tuhume-tuhumen aikata laifi da ake yi wa Mr Bankman-Fried.
A watan jiya ne kamfanin FTX ya gabatar da takardun karyewar jari a Amurka, abin da ya sa masu hada-hadar kirifto da yawa a kamfaninsa suka kasa janye kuɗaɗensu.
Shi ne kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na biyu mafi girma a duniya, inda yake cinikin kwabban kirifto na kimanin dala biliyan goma a kullum.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne kamfanin FTX ya shigar da takardun karyewar jari don samun kariya a ɗaya daga cikin karayar jari mafi girma a hada-hadar kuɗin kirifto, bayan masu hada-hada sun cire dala biliyan 6 daga kamfanin a cikin kwana 3 kuma abokin hamayyarsa Binance ya yi watsi da wata yarjejeniyar ceto FTX.